
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, tun da ya auri matarsa bai taba sayen ruwan Leda ba watau Pure Water.
Yace ruwan roba ake sha a gidansa.
Sannan kuma yace yana taimakonta hadda iyayenta amma ta zo tana zaginsa a idon Duniya
Gfresh ya bayyana hakane a yayin da yake nuna bacin ransa kan abinda ya kira da Butulci da matarsa ta masa inda take cewa zata kaishi wajan Hisbah ko ta sa ‘yan daba su dakeshi.