
Wannan bawan Allahn ya bayar da labarin yanda Mutanen Sabon Birni dake jihar Katsina suka sace iyalan Fulani ‘yan Bindiga bayan da Fulanin suka yi garkuwa da iyalansu.
Ya bayyana cewa, Fulanin sun nemi a yi Sulhu inda mutanen garin Sabon Birnin suka ce musu kawai su sako ya saki iyalan kowa.
Ya bayyana cewa, ‘yan Bindigar bayan sun saki mutanen kauyen sun basu hadda kudin motar zuwa gida.