
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa sabuwar dokar Haraji ta tanadi tsarin da zai nunawa Gwamnati yanda mutum ke kashe kudinsa.
Ta wannan hayar ne Gwamnatin zata san ainahin yawan kudin shigar mutum.
Shugaban kwamitin shugaban kasa akan Haraji, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi dashi.
Yace za’a bukaci mutum ya bayyana nawa yake samu kudin shiga a Shekara, amma idan mutum yayi Qarya, zasu gani ta hanyar yawan kudaden da yake kashewa.
Yace ta nan ne zasu fahimta kuma su nemi mutum ya biya kudin Haraji, yace idan mutum ki biya, zasu iya diba daga cikin asusun ajiyarsa na banki ba tare da an yi wani rikici dashi ba.
