
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya karɓi katin kasancewa ɗan jamʼiyyar ADC a mazaɓarsa ta Jada da ke jihar Adamawa.
Hakan ya kawo ƙarshen tsawon lokacin da ya ɗauka bai bayyana sauyin sheƙar ba, bayan da ya bar PDP.
Ya sanar da hakan ne a shafinsa na X, inda ya wallafa hotunan sa riƙe da katin sabuwar jami’yyarsa, da gajeren rubutu da ke nuna ya shiga jam’iyyar a hukumance.
A ranar 14 ga watan Yulin 2025 ne cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce ya fita daga PDP ba tare da ɓata lokaci ba.
Atikun ya kuma ce wajibi ne ya raba gari da jam’iyyar a yanzu bisa la’akari da yadda ta sauka daga harsashinta na asali.