Friday, December 5
Shadow

Fadar shugaban kasa tace ba zata yafewa Peter Obi ba saboda cewar da yayi da shine shugaban kasa zai amince Amirka ta kawo Khari Najeriya

Fadar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, ba zata yafewa Peter Obi ba saboda kalaman da yayi na amincewa da cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kawo Hari Najeriya.

Me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a rubutun da yayi a shafinsa na X inda yace ba zasu amince da kawo harin na Trump ba.

Peter Obi yace kamar mutum ne da iyalansa na fama da yunwa kawai sai wani ya kawo musu abinci, yace ai kamata yayi ya amince.

Yace to Najeriya abinda take bukata ne Amurka tace zata kawo mata ai kamata yayi kawai ta amince.

Karanta Wannan  FIFA ta goge Fastar gasar cin kofin Duniya ta 2026 data wallafa a shafinta bayan data sha suka saboda babu hoton Ronaldo a fastar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *