
Majalisar Dattijai ta bayyana cewa, ‘yan Bindiga da suka yi garkuwa da daliban makarantar MAGA dake jihar Kebbi, tserewa suka yi da suka ga jami’an tsaro.
Me magana da yawun majalisar, Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan a ganawa da manema labarai.
Yace ba’a biya kudin fansa ba kamar yanda ake yamadidi.
Yace kuma wai dan ba’a ga an kama kowa ba ko ba’a ga gawar wadanda suka yi garkuwa dasu din ba, hakan ba yana nufin ba’a yi fadan ba.
Yace sannan kuma Ba dole bane sai jami’an tsaro sun sanar da yanda suka kubutar da daliban ba, kawai dai ana son a kubutar dasu kuma an kubutar dasu din.