
Tauraron matashin mawakin Arewa, Bilal Villah na shan suka sosai bayan da ya nuna Bidiyon tsiraicin da ake zargin na tsohuwar Budurwarsa Amanine.
Bilal Villa ya nuna Bidiyon tsiraicin a wani Live da yayi akan Tiktok inda yake martani kan Bidiyon.
Saidai da yawa na cewa bai kamata yayi hakan ba dan kuwa idan akwai wanda zai rufawa tsohuwar Budurwar tasa asiri to shine.
Saidai a martaninsa kan cewa shine silar lalacewar rayuwarta, Bilal Villa yace shima a Media ya hadu da Amani.
