
Bidiyon Tauraron matashin mawakin Arewa, Bilal Villa a daji sanye da kayan sojoji ya bayyana a kafafen sada zumunta inda kuma aka ganshi dauke da Bindiga.
Lamarin ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke cewa ko da barkwanci ne hakan bai kamata ba musamman yanda ake cikin halin matsalar tsaro.
Babu dai tabbacin ingancin Bidiyon ko na gaske ne ko kuwa AI ne.
Saida a wani lamarin me kama da wannan, An kuma ga Bilal Villa a wani Bidiyo a daji sanye da kayan sojoji shima yana cewa suna daukar waka ne.
A karshen Bidiyon yace shi ba da Bindiga bane.