
Gwamnonin Arewa sun nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da ayyukan hakar ma’adanai na akalla watanni 6.
Sun ce harkar ma’adanai na taimakawa kara tabarbarewar harkar tsaro a yankin Arewa.
Gwamnonin sun kuma sha alwashin tara N228bn dan magance matsalar tsaro a yankin.
Kowace jiha da kananan hukumomin ta zasu samar da Naira Biliyan 1 inda a hakane za’a tara kudaden.
Hakanan sun goyi bayan samar da ‘yansandan jihohi.