Friday, December 5
Shadow

Shugaba Tinubu ya aika da sunan Dambazau da karin wasu mutane da zai baiwa Mukamin jakadanci zuwa majalisa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura ƙarin sunan mutum 4 ɗoriya a kan waɗanda aka fitar a baya zuwa ga majalisar dattawa domin a tantance su a matsayin jakadun ƙasar da za a tura ƙasashen waje.

Mutum huɗu da Tinubu ya tura su ne: Ibok-Ete Ekwe Ibas, tsohon shugaban riƙon-ƙwarya na jihar Rivers da tsohon ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau.

Sauran kuma su ne Sanata Ita Enang da tsohon gwamnan jihar Imo Chioma Ohakim.

Yanzu dai jimilla shugaban ya tura sunan mutum 65 ke nan da yake buƙatar majalisar ta tantance, inda ake sa ran da zarar an tantance su, zai sanar da ƙasashen da za a tura su.

Karanta Wannan  Yanzu-Yanzu: Kàsàr Amùrkà tà shìgà fàdàn Israyla da Ìràn tà aìkà dà manyan jiragen ruwa dauke da jiragen yaki gabas ta tsakiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *