
Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB dake tsare a gidan yarin jihar Sokoto bayan yanke masa hukuncin daurin rai da rai, Nnamdy Khanu ya bayyana cewa, ba zai iya zama a gidan yarin na jihar Sokoto ba.
Kanu ta hannun kaninsa, Prince Emmanuel Kanu, ya bukaci da kotun tarayya dake Abuja ta canja masa gidan yari.
Yace dalili kuwa shine zamansa a gidan yarin sokoto ba zai bashi damar daukaka kara da yake son yi ba.
Saidai me shari’a a kotun yace kanin na Nnamdi Kanu bashi da hurumin da zai iya shigar da wannan korafi, lauyane kawai ke da wannan hurumin.
Sannan Alkalin yace game da maganar daukaka kara ba lallai sai Nnamdi Kanu yayi da kansa ba, wakilansa, watau Lauyoyi zasu iyayi.