
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa, nada Christopher Musa ministan tsaro ya saka ‘yan Bindiga cikin damuwa.
Ya bayyana hakane yayin hirar da aka yi dashi a DCL Hausa.
Yace Christopher Musa mutun ne jajirtacce me kwarewa wanda kuma yasan aikinshi
Da aka tambayeshi ya zasu yi aiki tare, yace dama su ba bakin juna bane sun san juna tun suna matasa.