
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Rivers, Martin Amaewhule, ya sauya sheƙa tare da wasu ƙarin mambobi 15 na majalisar a ranar Juma’a, lamarin da ya ƙara dagula harkokin siyasar jihar wadda ke fama da rikice-rikicen cikin gida tun watanni da dama.
Rahotanni sun nuna cewa sauya sheƙar na da alaƙa da rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar.
Wannan mataki ya mayar da adadin mambobin majalisar da suka koma jam’iyyar APC zuwa 16 gaba ɗaya.
Sauya sheƙar ya faru ne a wani zama na musamman da majalisar ta yi inda mambobin suka bayyana cewa sun yanke shawarar komawa APC