
Tsohon Ministan shari’a a zamanin Mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Abubakar Malami ya bayyana cewa baya cikin masu daukar nauyin taaddaci a Najeriya.
Ya bayyana hakane a matsayin martani kan wani rahoto da ya zargeshi da wasu manyan Arewa da alaka da wasu da ake zargin masu daukar nauyin ta’addanci ne.
Malami yace a tarihinsa ba’a taba zarginsa ba ko aka kamashi ko aka masa shari’a akan daukar nauyin ta’addanci ba.
Yace ko tsohon Janar din da ya bayar da labarin ba yace yana zarginsu bane, yace an gano suna da alaka ne da mutanen da ake bincike.
Yace dan haka bashi da hannu a lamarin daukar nauyin ta’addanci a Najeriya.