
Sanata Natasha Akpoti ta ce dama irin damar da take son samu kenan wadda bata samu a bayaba ta tonawa sanata Godswill Akpabio asiri kan yanda ya nemi yin lalata da ita.
Ta bayyana hakane bayan da sanata Godswill Akpabio ya maka ta a kotu yana neman ta biyashi diyyar Naira Biliyan 200 saboda zargin ta bata masa suna da zargin karya data masa na cewa ya so yin lalata da ita.
Sanata Natasha Akpoti tace lallai ta samu sammacen kotu akan karar da Sanata Godswill Akpabio ya shigar akanta.
Tace yanzu ne ta samu damar tona masa Asiri.
A tace a baya abinda yasa bata tona masa asiri ba, a dokar majalisa sai ta gabatar da korafinta a gaban kwamitin bincike kamin taje kotu amma ba’a bata wannan damar ba amma yanzu ta ji dadi tunda da kansa ya kai magana kotu.