
Kasar Nijar ta fitar da sabuwar doka wadda tace daga yanzu duk wani abu da za’a shigar mata dashi dana Najeriya sai an masa daidai an ga komenene a ciki kamin a barshi ya wuce.
Nijar din ta fitar da wannan sabuwar sanarwar ne bayan da Najeriya ta dakile yunkurin juyin mulkin a kasar Benin Republic.
Hakanan sanarwar na zuwane bayan da kasar Burkina Faso ta rike jirgin saman Najeriya da sojoji 11 da suka shigar mata sararin samaniyar ta ba bisa ka’ida ba.
