
Rahotanni daga kasar Burkina Faso sun bayyana cewa, kasar ta ki yadda ta sako sojojin Najeriya 11 data kama da jirginsu C-130.
Rahoton yace kasar ta Burkina Faso ta dauke sojojin daga inda ta ajiyesu a baya inda a yanzu ta kaisu wani waje me matsanancin tsaro.
Kasar ta Burkina Faso ta yi imanin cewa sojojin na daga cikin wanda suka hana juyin Mulki a kasar Benin Republic.
Dan Jarida, Oseni Rufai ya bayyana cewa ya samu daga majiya me karfi cewa har zuwa yanzu Hukumomin Najeriya basu tuntubi kasar Burkina Faso kan sakin sojojin ba.
Najeriya dai tace sojojin na kan hanyar zuwa kasar Portugal ne jirgin su ya samu tangarda suka sauka a Burkina Faso.