Monday, December 15
Shadow

Kalli Bidiyon: Yanda matasan Daura suka rika yàgà Fastar Rarara yayin da ake masa Nadin Sarauta

Rahotanni sun bayyana cewa a yayin da Dauda Kahutu Rarara ya je Daura dan a masa nadin sarautar Sarkin Mawakan Hausa matasa a garin sun yi masa ruwan duwatsu.

Bidiyoyi na ta yawo a kafafen sada zumunta inda aka ga yanda matasa ke ta yaga fastar ta Rarara a Daura.

Rahotanni sun ce an yi ta jifarsa da tawagarsa da kyar suka sha.

A baya dai, Rarara ya yi baram-baram da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda dan Asalin Daura ne.

Karanta Wannan  HOTUNA: Yadda Ruwan Sama Ďa Iska Mai Ķarf Ya Kwaye Saman Gidaje Da Ajujuwan Makarantu A Karamar Hukumar Mayo Belwa Dake Jihar Adamawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *