
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya kalubalanci masu zarginsa da hannu akan matsalar tsaro da su tafi kotu.
Ministan ya bayyana hakane a wata hira da DLC Hausa ta yi dashi inda yace zargin fatar baki idan ba kotu ce ta tabbatar dashi ba na banza ne.
Zarge-zarge dai sun yi yawa akan Ministan inda da yawa suke kiran da ya sauka daga mukamin nasa.