
Najeriya ta aika da wakilai na musamman zuwa kasar Burkina Faso dan a tattauna yanda za’a sako sojojin Najeriya 11 da jirginsu C-130.
Wadanda aka aika din daga ma’aikatar harkokin kasashen waje ne da kuma ma’aikatar tsaro ta kasa.
Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya jagoranci tawagar.
Zasu tattauna maganar sasanci tsakanin kasashen biyu da kuma inganta tsaro.