Saturday, June 27
Shadow

Buhari har yayi Mulkinsa ya gama bai kama kowa ba, kuma baisa a kama kowa ba>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai kama kowa ba kuma bai sa a kama kowa ba har yayi mulkinsa ya gama.

Ya bayyana hakane a martanin da yakewa Dawisu, Watau Salihu Tanko Yakasai da yace Buhari ya kamashi.

Bashir yace idan dai Dawisu zai ce an kamashi a zamanin Mulkin Buhari zai yadda amma maganar cewa Buhari yasa an kamashi ba gaskiya bane.

Karanta Wannan  Zanga-zangar kin jinin Donald Trump ta barke a biranen kasar Amurka bayan da ya lashe zabe, Kalli Hotuna da Bidiyon yanda Amurkawa da yawa ke kuka saboda takaicin ya ci zabe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *