
Diyar tsohon shugaban kasa, Halima Buhari ta bayyana cewa, Mahaifinsu yana sane da cewa, mutane da yawa basu ji dadin mulkinsa ba kuma sun rika sukarsa.
Ta bayyana hakane bayan wallafa littafi akan tarihin rayuwar tsohon shugaban kasar.
Tace duk da yake akwai wanda suka godewa shugaban kasar saboda irin yanda rayuwarsu ta canja, amma tabbas akwai da yawa wanda basu dadin mulkin mahaifin nata ba.