Sunday, March 8
Shadow

Hukumar ‘yansandan kasar Ghana ta gargadi matan aure cewa duk matar data hana mijinta mu’amalar aure, Zata fuskanci hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari

Jami’in Hukumar ‘yansandan kasar Ghana, (ACP), Dennis Fiakpui yace takura a aure da saka damuwa babban laifine a kasar.

Yace a tsakanin ma’aurata, duk wanda ya hana dan uwansa ma’amalar aure, misali mace ta ki yadda da mijinta a gado, idan ya kai kara kuma kotu ta samu matar da laifi, zata fuskanci hukuncin daurin shekaru 2 a gidan yari.

Yace hakanan itama idan macence mijinta baya kwanciyar aure da ita, zata iya kaishi kara a nema mata hakkinta.

Yace hakanan idan miji na dadewa a waje baya komawa gida da wuri ko kuma ya daina cin abincin matarsa, duka zata iya kaishi kara a bi mata hakkinta.

Karanta Wannan  An gudanar da taron masu ruwa da tsaki na PDP dan shawo kan matsalar masu ficewa daga jam'iyyar zuwa APC, kuma Wike ma ya halarci wajan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *