
Rahotanni sun ce ganga kusan miliyan 20 na danyen man fetur din Najeriya da ake son sayarwa a tsakanin watannin Disamba zuwa January har yanzu yana nan ba’a sayar dashi ba.
Kafar Reuters tace itama kasar Angola danyen man nata nacan Jibge an kasa sayar dashi.
Rahoton yace kasashen biyu na ta kokarin ganin sun samu masu sayen danyen man fetur din nasu amma abu ya faskara.
Rahotanni sun ce kasar China wadda tana daya daga cikin manyan masu sayen danyen man na kasashen Afrika ta fara komawa sayen man daga kasashen Larabawa saboda yafi saukin farashi da kuma saukin sufuri.