A yayin da rikici yaki karewa tsakanin Masu martaba, Muhammad Sanusi II da Aminu Ado Bayero, an kawo wata shawara da zata iya zama mafita ga lamarin.
An bada shawarar cewa a hada sarakunan biyu wanda kowanne ya doge akan bakarsa shine sarkin Kano a basu musabakar karatun Qur’ani.
Duk wanda yaci sai a bashi sarautar Kano.
Shafin Kwankwasiyya ne ya kawo wannan shawara.
Sarki Muhammad Sanusi II dai shahararren malamin addini ne wanda yana tafsiri kuma shine ke hudubar juma’a.
Idan dai za’ yi wannan musabaka, ga dukkan alamu shine zai yi nasara.