
‘Yan Kwallon kasar Misra/Egypt sun karanta Fatiha da suratul Ikhlas sau 3 a dakin canja kaya kamin wasansu da kasar Zimbabwe a ci gaba da gasar AFCON.
Bidiyon nasu ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta inda musamman musulmai suka rika musu fatan Nasara.
Kuma sun yi nasara a wasan inda Egypt taci 2 Zimbabwe taci 1