
Tauraruwar Tiktok, Habiba Dorayi ta bayyana cewa tun dambarwar da aka yi a kwanakin baya har aka kama ta ta daina hawa Bidiyo tana maganganun batsa.
Tace amma wasu na amfani da hotunanta a Facebook suna dora maganganun batsa.
Tace su ji tsoron Allah su daina ko kuma ta barsu da Allah ya isa.