
Kailani Muhammad wanda ya fito ya bayyana rashin jin dadi game da abinda Dangote yawa Farouk Ahmed sannan yace shi Dangoten ma ya kamata ya fito ya gaya musu yanda ya samu kudinsa a Fatakwal.
Saidai Maganar batawa Dangote dadi ba inda ya fito yace Kailani Muhammad ya fito ya janye kalamansa sannan ya bashi hakuri idan ba haka ba zai makashi a kotu ya nemi ya biyashi diyyar Biliyan 100.
Hakan yasa Kailani Muhammad ya fito ya janye kalaman nasa tare da baiwa Dangoten hakuri.