YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano Ta Umarci ‘Yan Sanda Da Su Fitar Da Aminu Ado Bayero Daga Gidan Sarki Na Nassarawa dan rusheshi a gina wani.
Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta ce za ta fara aikin rushe katangar gidan Sarki na Nasarawa da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ke ciki, tana mai cewa “saboda ya lalace”.
Gwamnatin ta kuma umarci kwamishinan ‘yansandan jihar da ya fitar da Aminu Ado daga gidan bayan hukuncin kotu a yau Alhamis, wanda ta yi iƙirarin cewa ya ba ta nasara a kan ɓangaren da suka shigar da ƙarar.
Kwamashinan Shari’a na Kano Haruna Isa ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a gidan gwamnati, inda ya jaddada cewa bangon ƙaramin gidan sarkin da ke ƙwaryar birnin Kano ya lalace.
“Mun kammala shirye-shirye domin rushewa da kuma sake gina katangar da ta lalace nan take,” in ji shi
Menene ra’ayinku?
[…] jiyane dai rahotanni suka bayyana cewa, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin rushe fadar Nasarawa wadda sarki Aminu Ado Bayero ke ciki da nufin […]