Fasto Adeboye ya roki Mabiyansa cewa su yiwa Allah idan yayi kuskure su daina dauka suna zuwa suna yadawa a kafafen sada zumunta.
Yace maimakon haka duk wanda yaji yayi kuskure ya je ya sameshi ya gyara masa, yace babu wanda yafi karfin yin kuskure.
A baya dai, Bishop Oyedepo ya taba cewa an gayyaceshi kasar Amurka a watan Janairu ana tsananin Sanyi amma ya roki Allah aka daina sanyin aka koma zafi saboda baya son sanyi kuma yana dawowa Najeriya sai aka ci gaba da sanyin da ake a kasar Amurka.
Hakanan ya taba cewa akwai wata mata da aka yankewa nonuwa saboda cutar kansa amma data shafa wani kyalle da yawa addu’a, sai nonon nata ya sake fitowa.