
Rahotanni daga kasar Ghana sun bayyana cewa, Hukumar ‘yansandan kasar sun kama fastonnan me suna Evans Eshun da yace wai za’a yi tashin Qiyama ranar 25 ga watan Disamba, watau ranar Kirsimeti.
Hukumar ‘yansandan ta ce bata yadda da masu amfani da addini suna tayarwa da mutane hankali ba inda tace tabbas an kama Fasto Evans Noah.
Saidai bata bayyana laifukan da ake zarginsa da aikatawa ba.
Fasto Evans Noah yace wai an masa wahayin za’a yi tashin Qiyama ranar 25 watan Disamba sannan an bashi Umarnin sassaqa jirgin ruwa irin na Annabi Nuhu saboda wai za’a yi ruwan sama.
Saidai daga baya da ranar Kirsimeti ta zo ba’a yi tashin qiyamar ba, ya bayyana cewa shi ranar kawai aka sanar dashi, ba’a sanar dashi shekarar da za’a yi tashin qiyamar ba.