
Malamin addinin Islama, Sheikh Salihu Zaria ya yi karin haske kan Harin da ake cewa an kai masa saboda yayi magana akan Haraji.
Malamin yace ba gaskiya bane, ba’a kai masa hari ba.
Yace har ma Karatu yayi, dan haka masu cewa, an kai masa Hari karya suke.
Yace kuma sune suka tallata gwamnatin Musulim Muslim kuma a yanzu bata abinda ya kamata dan haka dole su fito su fada.