
Hukumar sojojin Najeriya ta bukaci mutanen jihar Sokoto da su dawo da baraguzan bama-bamai wanda kasar Amurka ta Jefa.
Rahotanni sun ce wasu ‘yan gwangwan sun kwashe baraguzan bama-baman da Amurka ta jefa a jihar.
Saidai hukumar sojojin Najeriya tace mutane su dawo da wannan baraguzan Bama-baman dan akwai ma wanda basu tashi ba dan kada su cutar da mutane.
Hukumar sojojin ta nemi hakanne ta bakin kakakin hukumar a yayin da yake ganawa da manema labarai.