
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi martani kan abin kinyar da ake zargin shugaban da yi ta hanyar wallafa Hoton AI a shafinsa na X.
Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya bayyana cewa, Hoton bana AI bane.
Yace da gaske shugaba Tinubu da Takwaransa, Paul Kagame suna kasar Faransa kuma sun gana.
Yace wanda ya daukesu hotonne wayarsa bata daukar hoto me kyau shine yayi Amfani da AI ya gyara hoton.
Lamarin hoton dai ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta.