Monday, December 16
Shadow

Nasiha ga masoyiyata

Masoyiyata ki rike karatu na Boko dana Islamiyya, Allah ya sanya miki Albarka a rayuwa.

Masoyiyata ki yiwa iyayenki biyayya da neman Albarkarsu, ki gujewa abinda zai bata musu rai.

Masoyiyata ki rika Istigfari dan kullun cikin sabo muke, kuma ki rika salati ga Annabi dan neman hasken rayuwa da ceto a Duniya da Lahira.

Masoyiyata ki rika karatun Qur’ani dan fita daga kunci da neman biyan bukata da farin cikin Duniya da lahira.

Masoyiyata ke kyakkyawace, maza da yawa, masu niyya me kyau da masu mummunar niyya zasu ta kawo miki hari, kada ki yadda da duk wani wanda burinshi kawai ya taba jikinki.

Karanta Wannan  Jerin sunayen masoya

Masoyiyata, ki kula, kada ki bi rudin zamani waja bayyana surar jikinki, Allah ya miki daraja da kima kada ki zubar da ita a titi wajan yin shigar banza wadda zata jawo miki shedanun mutane da Aljanu.

Masoyiyata ina sonki da gaskiya, so wanda nake fatan ya kaimu ga aure, ina miki nasiha akan kada ki biyewa rudin samarin zamani masu dadin baki, masu karya da kudi, ko sutura, ki zabi me sonki tsakani da Allah.

Masoyiyata ki rika neman tsari da ga shaidan a duk sanda kika ji fushi.

Masoyiyata kada ki biyewa kawayen banza, duk wadda kika ga zata sakaki a hanyar banza, ki mata nasiha, idan ta ki, to ki gujeta.

Karanta Wannan  Hirar soyayya

Masoyiyata kada ki yadda ki kaiwa Saurayi ziyara dakinsa, wannan ba dabi’ar mata na gari bace, hakan zai iya kaiwa ga aikata alfasha.

Masoyiyata idan zai yiyu, kada ki roki saurayi ya baki wani abu, saidai idan da kanshine yaso yi miki kyauta, ki roki mutanen da suka zama dole a gareki, mahaifi, mahaifiya, wa ko kani.

Masoyiyata kada ki zama me tsiwa, kada ki rika daga murya da sunan wayewa, ki zama me kamun kai, ko da an zageki, kada ki rama, saboda kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *