
Rahotanni daga Kano sun bayyana cewa, dan jagoran Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso me suna, Mustapha wanda kwamishinan matasa da wasannine zai ajiye aikinsa.
Hakan na zuwane bayan da Abban ke shirin komawa jam’iyyar APC.
Rahoton yace ba Mustapha Kwankwaso ne kadai zai ajiye aikin nasa ba, hadda karin wasu kwamishinoni dake aiki tare da gwamnatin Kanon.
Rahotanni sun bayyana cewa, Dangantaka ta yi tsami tsakanin Abba da Kwankwaso tun bayan data bayyana a zahiri cewa Abba zai koma jam’iyyar APC.