
Tauraron mawakin Kasar Senegal, Akon ya harlarci wasan da kasarsa ta buga da kasar Mali.
Wasan ya kare Senegal na cin 1-0.
An ga Akon ya tashi yana murna bayan da Ndiaye yaciwa Senegal Kwallon da ta basu nasara inda ya rika cewa dama ya fada.
Bayan Wasan an ga Akon da Sadio Mane suna gaisawa inda Akon ke cewa, zai kasance tare dasu har su yi nasara.