
Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa, ba zata baiwa Dr. Rabiu Musa Kwankwaso takara a zaben shekarar 2027 ba.
Jam’iyyar ta bayyana hakane ta bakin sakataren ta, Mr. Ogini Olaposi a sanarwar da ya fitar ranar 12 ga watan Janairu.
Ya bayyana cewa jam’iyyar zata baiwa asalin ‘yan jam’iyyar masu kishinta takara ne.
Hakan na zuwane biyo bayan rashin jituwar da aka samu tsakanin Kwankwaso da jam’iyyar ta NNPP.