
Dan gidan Ministan ayyuka, Osborn Umahi ya fito takarar neman kujerar shugaban karamar hukumar.
Ya fito ne neman takarar kujerar Karamar hukumar Ohaozara ta jihar Ebonyi.
Magoya bayansa ne suka rakashi Ofishin APC inda ya sayi fom din takarar akan Naira Miliyan 30.
Dama dai a baya yawa mahaifinsa shugaban yakin neman zabe sannan kuma gwamnan jihar Ebonyi na yanzu, Francis Nwifuru ya bayyana shi a matsayin dan takararsa