
Shugaban kasar Senegal ya jinjinawa ‘yan wasan kasarsa bayan da suka yi nasarar daukar kofin AFCON.
Ya bayyana cewa sun basu aiki kuma sun gudanar da aikin yanda ya kamata.
Senegal ta doke me masaukin baki, Morocco da ci 1-0 inda hakan ya bata damar lashe kofin na AFCON.
Shugaban yace ‘yan wasan nasa sun yi wannan nasara ne duk da kalubalen da suka rika fuskanta.