
Dan Atiku Abubakar, Abba Atiku da ya koma jam’iyyar APC ya dauki hankula bayan jawabin daya gabatar na farko bayan komawarsa APC.
An ga Bidiyon sa yana cewa, duk wani me goyon bayansa ko wanda suke karkashinsa su daina goyon mahaifinsa, Atiku Abubakar su koma goyon bayan shugaba Tinubu.
Saidai wani abu na daban da ya kara daukar Hankula akan Abba Atiku shine yanda aka ga yana magana, baya iya tsayawa da kyau.
Da yawa sun yi zargin cewa yana shaye-shaye.


