Wednesday, April 15
Shadow

Kuma Dai: Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya sake maka ICPC a kotu inda yake neman su biyashi diyyar Naira Biliyan 15.6

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya maka hukumar yaki da rashawa, ICPC a kotu inda yake neman su biyashi diyyar naira Biliyan 15.6 saboda bata masa suna.

Hakan na zuwane yayin da ICPC tace ta gano na’urar yiwa waya kutse a gidan malam Nasiru Ahmad El-Rufai.

Lauyoyin Malam Nasiru sun ce kalaman na ICPC abin damuwa ne kuma sun bata masa suna

Dan haka El-Rufai yace wannan abu ya take masa hakkinsa na Bil’adama inda yace yana neman.

Biliyan 15.6 na bata masa suna.

El-Rufai yace ya baiwa ICPC awanni 24 su gaggauta biyansa wannan kudi in ba haka ba zai makasu kotu.

Karanta Wannan  Gwammatin Najeriya ta amince mana kamin Khàrìn da muka kai Sokoto>>Inji Kasar Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *