
‘Yan Najeriya na nuna fushinsu bayan zargin shugaban hukumar tattara Haraji ta kasa, Zach Adedeji ya saka agoguna masu tsada.
Wasu hotunansa guda biyu sun bayyana inda aka ganshi sanye da agoguna kirar Patek Philippe daya farashin ta Naira Miliyan 91,898,970 inda kuma dayar farashinta Naira Miliyan 157,905,530.
Saidai masu kareshi sun bayyana cewa dama can me kudi ne.
Da yawa dai na cewa zasu biya haraji amma ba zasu lamunci a rika satar musu kudi ba.