
Malam Bashir Haruna Dorayi Chiranchi da akawa iyalansa aika-aika a jihar Kano, Ya bayyana cewa, ya bayar da gidansa kyauta ga Gwamnatin jihar Kano dan a gina Islamiya.
Ya bayyana hakane yayin da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya je masa ziyarar gaisuwa.
A wajan Gwamnan Kano yace Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin rayuwarsa gaba daya.