
Malam Abdulrahman Umar Sautussunnah ya baiwa matasa shawarar cewa idan suna son mallake zuciyar ‘yan matansu, sai sun hada da yin kyauta.
Ya bayyana cewa, akalla, idan kana son ka mallake Zuciyar budurwar ka to ka rika mata kyautar Naira Dubu 10 duk sati, ko kuma kyautar Naira dubu 5 duk sati idan baka da karfi.
Yace idan kuwa baka yi, za’a samu wani da zai rika mata kyauta ta maka kwace.