Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, an kama ‘yan fashin da suka kashe janar din soja mai ritaya a Abuja.
An kama mutanen su 4 wanda aka bayyana sunayensu kamar haka:
Ibrahim Rabiu, 33; Nafiu Jamil, 33; Aliyu Abdullahi, 47; Mohammed Nuhu, 28
Rahoto yace dukansu suna zaunene a Apo Primary school.
Kuma duka sun amsa laifin da ake tuhumarsu dashi.
Sunce aun kashe Brig.-Gen. Uwem Udokwere Ne bayan da suka ga ya fito da Bindiga yana shirin harbinsu.
Kuma sun sace wayarsa da sauran wasu kayan amfani a gidan nasa.
Ranar Asabar data gabata ne dai maharan suka yi wannan mummunar ta’asa wadda ta dauki hankula a Najeriya.