Friday, July 17
Shadow

Da Duminsa:Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya aikawa kotu da korafi kan wata Mugunta da take hakkinsa da ake masa a ofishin ICPC

Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya aikewa da kotun Magistrate dake Abuja da korafin cewa, ana kokarin take masa hakkinsa a matsayinsa na dan kasa.

ElRufai yayi zargin cewa, shugaban Hukumar ICPC din Musa Adamu Aliyu ta hannun wasu yaransa ya bayyana masa cewa sharadin sakinsa shine sai idan ya amince zai daina shiga harkar siyasa.

El-Rufai ta hannun Lauyansa yace wannan kokarine na take masa hakkinsa a matsayinsa na dan kasa wanda ba zai lamunta ba.

Zuwa yanzu dai Hukumar ta ICPC bata ce uffan ba kan zargin da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya mata.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Idan kuka ganni Ina Saka Hotuna ko Bidiyon Tsyraychi ko kuka ga ina Aikata Alfasha da wani kada wanda ya sake min gargadi ko yace inji tsoron Allah saboda na dade ina rokon a Taimakeni dan Allah babu wanda ya kulani, dan haka zan ci gaba da bada jikina>>Inji Maryam Buzuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *