
Kotu tace doka ta baiwa ‘yan Najeriya damar daukar ‘yansanda Bidiyo yayin da suke gudanar da aiki.
Babbar Kotun tarayya dake Warri, Jihar Delta ce ta yi wannan hukuncin.
A karkashin mai shari’a, Justice H. A. Nganjiwa inda tace ‘yan Najeriya na da damar daukar ‘yansanda Bidiyo yayin da suke aiki a bainar jama’a.
Sannan ta baiwa wanda ya shigar da karar, Maxwell Uwaifo nasara akan ‘yansanda nasara inda tace a biyashi diyyar Naira Miliyan 5 sannan a bashi wata Naira Miliyan 2 dan ya biya kudin daukar lauya da wahalhalun karar da ya shigar.