Thursday, April 2
Shadow

Ban taba ganin Azzalumai irin su Atiku da Kwankwaso, da El-Rufai ba, Ta yaya zasu zo su iskeni a gidana suce zasu yi fada dani kuma su yi nasara>>Inji Wanda yace shine shugaban ADC ba David Mark ba watau Nafiu Bala

Wanda ke ikirarin cewa shine shugaban jam’iyyar ADC, Nafiu Bala wanda kuma ya kai su Atiku, Kwankwaso, Peter Obi, da David Mark, da Rauf Aregbesola da sauransu kotu yana neman a kwace shugabancin jam’iyyar a bashi watau Nafiu Bala yace bai taba ganin zalunci irin na su Atikun ba.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi wadda ta watsu a kafafen sada zumunta.

Yace ta yaya mutane zasu zo har gidansa su sameshi suce zasu yi fada dashi kuma su yi nasara?

Karanta Wannan  Direban Adaidaita Sahu Ya Kare Da Sakamako Mafi Daraja A Jami'ar Bayero Dake Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *