Wednesday, April 15
Shadow

Tattalin arzikin Najeriya zai samu habaka fiye daga kasashen Amurka, Ingila, da Jamus>>Inji Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa, ta bayyana cewa, Tattalin arzikin Najeriya zai samu habaka sosai fiye dana kasashe masu arziki irin su Amurka, Ingila, da Jamus.

Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X inda yake martani kan bayanan habakar tattalin arziki da kungiyar bayar da lamuni ta Duniya, IMF ta fitar.

IMF tace Najeriya zata samu habakar tattalin arziki da maki 4.1 a shekarar 2026.

Wannan maki yafi na kasar Amurka wanda IMF tace 2.3 ne sannan yafi na kasar Ingila wanda IMF tace 0.8 ne hakanan yafi na kasar Jamus wanda shima 0.8 ne.

Karanta Wannan  Babu tsageran da ya fi karfin mu a kasarnan>>Inji Janar din Soja

Daniel yace Gwamnatin Tinubu ba da wasa take ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *